Isa ga babban shafi

In ban da nasarorin da na samu a baya da tuni Liverpool ta kore ni- Klopp

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Jurgen Klopp ya bayyana cewa ya na rike da aikinsa ne kawai saboda nasarorin da ya kai Club din ga samu a baya amma ba saboda halin da kungiyar ke ciki a wannan kaka ba.

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, Jurgen Klopp
Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, Jurgen Klopp POOL/AFP
Talla

Jurgen Klopp dan Jamus da ke wannan batu gabanin tattakin Liverpool zuwa gidan Chelsea a yau talata, ya ce idan da wannan ce kaka ta farko da ya karbi ragamar Liverpool aka samu wannan matsala, ko shakka babu da yanzu wani batu ake yi daban.

Bayan korar Brendan Rodgers da Graham Potter a lahadin da ta gabata, hankula sun koma kan Jurgen klopp wanda shi ma kungiyar ke ganin mafi munin kaka a tarihi, dai dai lokacin da sai a badi ne kwantiraginsa zai kare.

Zuwa yanzu dai manajojin firimiya 13 aka kora cikin wannan kaka kadai, wanda ke da nasaba da rashin katabus din kungiyoyinsu a gasar ta firimiyar Ingila.

Klopp dan Jamus me shekaru 55 cikin shekaru 7 da rabi da ya shafe yana horar da Liverpool ya taimakawa kungiyar samun tarin nasarorin da ta shafe shekaru tana kishirwarsu ciki har da kofin Firimiya, zakarun Turai, FA, Carabao da club world Cup da dai sauran muhimman kofuna.

Klopp, wanda ya karbi aikin horarwar a 2016 daga hannun Rodgers ya ce masu kungiyar ta Liverpool sun lura da yanayin da ake ciki kuma sun yi masa uziri amma hakan ba ya nufin zai zuba ido ba tare da yin kokarin samar da sauyi ba.

Klopp dai na fatan ganin ya kammala gasar ta Firimiya a sahun ‘yan hudun saman teburi don kaucewa samun kansa a Europa sai dai akwai bukatar maki 8 kafin kaiwa wannan mataki dai dai lokacin da wasanni 11 ya rage a kammala gasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.