Messi ya zarce Ronaldo a yawan cin ƙwallaye a lik din Turai da kwallo 702
Lionel Messi ya zarce abokin hamayyarsa Cristiano Ronaldo a yawan cin ƙwallaye a lik ɗin Turai, bayan da ya ci ƙwallo na 702 a lik ɗin Turai, bayan wasan da Paris St Germain ta doke Nice da ci 2-0 har gida a wasan Ligue 1 na Faransa ranar Asabar.
Wallafawa ranar:
Messi ne ya budewa PSG ci a wasan na ranar Asabsar kafin Sergio Ramos ya ƙara na biyu minti 14 kafin a tashi wasan.
Da wannan sakamako, PSG ta ci gaba da jan ragamar teburin gasar ligue 1 na Faransa da maki 69, tazarar maki shida tsakaninta da Lens dake biye da ita.
Tun bayan komawa PSG daga Barcelona a shekarar 2021, Messi ya ci kwallaye 30 kuma mika na ci 32, ko a wasan na ranar Asabar ma shi ne ya bai wa Ramos ya ci na biyu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu