Isa ga babban shafi

Ronaldo ya kafa tarihin zama dan wasa mafi dokawa kasar sa wasa

Cristiano Ronaldo ya kafa tarihin zama dan wasa mafi dokawa kasar sa wasa lamarin da ke goge duk wani tarihin dan wasa a yawan wasannin da ya dokawa kasarsa, bayan da a daren jiya ya dokawa Portugal wasa na 197 tare da zura kwallaye 2 a wasannin neman gurbin shiga gasar EURO2024 da kasashen Turai ke ci gaba da dokawa.

Cristiano Ronaldo sanye da rigar wasan Portugal.
Cristiano Ronaldo sanye da rigar wasan Portugal. REUTERS - JOHN SIBLEY
Talla

Yayin wasan na jiya wanda Portugal ta yi nasara kan Liechtenstein da kwallaye 4 da nema Joao Cancelo ya bude da kwallaye biyu na farko gabanin Ronaldo ya zura ta 3 a bugun fenariti kana ya karkare da wata kwallo daban.

Cristiano Ronaldo mai shekaru 38 wanda Portugal ta cire daga tawagar farko yayin gasar cin kofin Duniya da ake ganin shi ya haddasawa kasar ficewa daga gasar cikin sauki bayan shan kaye da kwallo 1 mai ban haushi a hannun Morocco, kwallayen da ya zura a jiya na matsayin kwallo ta 120 da ya zurawa kasarsa.

Dama dai Ronaldo na da tarihin zama dan wasa na farko da ya fara zurawa kasarsa kwallaye 100, yayinda yanzu kuma ya sake zama dan wasa mafi dokawa kasarsa wasa.

Ronaldo yayin wasannin gasar cin kofin Duniya a Qatar.
Ronaldo yayin wasannin gasar cin kofin Duniya a Qatar. AP - Petr David Josek

A zantawarsa da manema labarai bayan tashi daga wasan, Ronaldo wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or sau 5, ya ce fatansa shi ne zama dan wasa mafi dokawa kasarsa wasa, domin kuwa baya fata nan kusa ya dakata da dokawa Portugal wasa.

 

A cewarsa kafa tarihi ya ba shi kwarin gwiwar ci gaba da nuna hazaka.

A shekarar 2003 ne Ronaldo ya fara dokawa Portugal wasa kuma ya zama dan wasa na farko a tarihi da ya taba zura kwallaye a mabanbantan gasar cin kofin Duniya har guda 5 yayin gasar da ta gudana a Qatar.

Ronaldo wanda yanzu haka ke taka leda da kungiyar Al Nassr ta Saudiya bayan katse kwantiraginsa da Manchester United anga yadda ya bar fili yana zubar da hawaye bayan fitar da Portugal daga gasar cin kofin Duniya, wasan da ya kalle shi daga benci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.