Isa ga babban shafi

Mahaifin Messi 'ya gana da shugaban Barca kan batun komawarsa Camp Nou

Mahaifin Lionel Messi kuma wakilinsa Jorge ya gana da shugaban kungiyar Barcelona Joan Laporta a watan da ya gabata, daidai lokacin da ake ta cece-kuce kan makomar dan wasan mai shekaru 35 a Paris Saint Germain.

Dan wasan PSG Lionel Messi
Dan wasan PSG Lionel Messi AP - Aurelien Morissard
Talla

Rahotanni suka ce Messi na dari-darin sabanta yarjejeniyarsa da PSG, abin da ya as ake alakanta shi da komawa kungiyar ta Catalonia a bazara.

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta fito fili ta amince da bukatar dawo da Messi a filin wasa na Nou Camp, inda mataimakin shugaban club din Rafael Yuste ya bayyana cewa kungiyar na zawarcin dawowarsa.

Ganawar Jorge da Laporta ya kara fito da batun a fili, to sai dai jaridar The Mirror ta ruwaito cewar, ganawar bata da alaka da batun sauya shekar Messi.

Wasa ta musamman

Mirror ta bayyana cewa ganawar da Jorge ya yi da Laporta ta shafi wani wasa na musamman da ake shrin gudanarwa a Camp Nou domin karrama Messi da zarar ya kammala wasan kwallon kafar Turai.

Sai dai Mirrow tace, babu yadda wadannan mutunen zasu gana ba tare da tattauna batun komawar Messi zuwa Barca ba.

Lionel Messi yayin murnar zura kwallo da aboakan wasansa Kylian Mbappé da Presnel Kimpembe yayin wasan Ligue 1
Lionel Messi yayin murnar zura kwallo da aboakan wasansa Kylian Mbappé da Presnel Kimpembe yayin wasan Ligue 1 AP - Christophe Ena

A karshen watan Yuni Kwantiragin Messi zai kawo karshe da PSG kuma akwai rashin tabbas kan inda zai buga wasa a kakar wasa mai zuwa.

Tsamin dangartakar Messi da Laporta

Komawa filin wasa na Nou Camp, inda ya kwashe mafi yawan rayuwarsa ta taka leda, abu ne mai yiyuwa duk da akwai tsamin dangantaka tsakanin dan wasan mai shekaru 34 da Laporta.

Rashin jituwar da ke tsakanin su ya fito file ne lokacin bukin bayar da kyaututtuka ta FIFA a watan Fabrairu lokacin da suka kauce wa juna.

Messi ya ci wa kungiyar PSG ta Christophe Galtier kwallaye 34 a kakar wasa ta bana, 25 daga cikin ya zura ne wasannin gasar Ligue 1 da kuma bakwai a gasar zakarun Turai.

Messi ya ci kwallaye masu yawa a Barcelona

A lokacin yana Barcelona Messi ya ci kwallaye 672 kuma ya tabbatar da matsayinsa na daya daga cikin manyan ‘yan wasa da aka taba samu a duniyar tamola.

Idan Messi ya koma Barcelona to zai yi wasa ne a karkashin Xavi, wanda tsohon abokin wasan sa ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.