Isa ga babban shafi

Juventus ta juya baya ga shirin kirkirar sabuwar gasar Super League

Kungiyar Juventus ta fara shirin ficewa daga shirin kirkirar sabuwar gasar gwallon kafar Super League da za ta kunshi manyan kungiyoyin kwallon kafar nahiyar Turai guda 8. 

Tambarin kungiyar kwallon kafa ta Juventus.
Tambarin kungiyar kwallon kafa ta Juventus. © goal
Talla

Matakin na Juventus ya bayyana ne, bayan wasikar da ta aike wa Real Madrid da Barcelona akan bukatar su tattauna kan aniyar da ta kulla na janyewa da gagarumin shirin kafa sabuwar gasar a Turai. 

A watan Oktoban 2021 ne shirin kafa gasar Super League ya fara rushewa, bayan da akasarin manyan kungiyoyin da suka kulla yarjejeniyar suka janye, sai dai tun waccan lokacin Juventus, da Barccelona da kuma Real Madrid suka tsaya kai da fata kan cewar za su cigaba da kokarin cimma burin ganin kafuwar sabuwar gasar. 

Watannin baya bayan nan dai basu yi wa Juventus dadi ba la’akari da hukuncin hukumar kwallon kafar Italiya da ya soke mata maki 15 a gasar Seria A, bayan laifin almundahana a cinikin ‘yan wasa da kuma kashe kudade da aka samu kungiyar da aikata wa. 

Bayan wasu ‘yan makwanni dai an soke hukuncin kwacen makin, sai dai bayan sake sauraren karar, hukunci na biyu  ya sake kwacce wa Juventus maki 10, matakin da kungiyar ta amince da shi. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.