Isa ga babban shafi

Barcelona kadai zan iya taka wa leda a Turai bayan PSG - Messi

Lionel Messi ya ce manyan kungiyoyin Turai da dama sun yi tayin kulla yarjejeniya da shi amma ya yi watsi da su, kafin yarjejeniyar da ya kulla da Inter Miami da ke gasar kwallon kafar Amurka.

Lionel Messi
Lionel Messi AP - Aurelien Morissard
Talla

Dan wasan ya ce kungiya daya tilo kawai da zai iya kulla yarjejeniya da ita bayan rabuwarsa da Paris Saint Germaine ita ce Barcelona.

A karshen watan nan na Yuni yarjejeniyar Messi da PSG za ta kare bayan shafe shekaru biyu da yayi a birnin Paris.

A tsawon lokacin da ya dauka yana haska wa a Faransa, Messi ya ci wa PSG kwallaye 32, cikin wasanni 75 da ya buga wa kungiyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.