Messi ya kafa tarihin zura kwallo cikin sauri a wasan Argentina da Australia
Lionel Messi ya zura kwallo mafi sauri a tarihin yawan kwallayen da taba zurawa Argentina yayin wasan da kasar ta shi ta lallasa Australia da kwallaye 2 da nema.
Wallafawa ranar:
A minti na 1 da sakanni 16 da fara wasa ne Messi ya zurawa Argentina kwallonta na farko yayin wasan sada zumuntar da ya gudana a birnin Beijing na China, wanda ke matsayin kwallo mafi sauri da dan wasan mai shekaru 35 ya taba zurawa kasarsa cikin sauri.
Wasan na jiya dai shi ne karon farko da Messi ke dokawa Argentina tun bayan komawarsa Inter Miami ta Amurk da taka leda.
Haka zalika wannan ne wasa na farko da tawagar karkashin jagorancin Lionel Scaloni ke dokawa tun bayan lashe kofin Duniya a watan Disamban bara can a Qatar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu