Isa ga babban shafi

Gundogan zai koma Barcelona daga Man City a kyauta

Kyaftin na kungiyar kwallon kafa ta Manchester City Ilkay Gundogan zai canza sheka zuwa Barcelona a kyauta, bayan ya karkare kwantiraginsa a karshen wannan wata.

Dan wasan tsakiya na Man City  Ilkay Gundogan.
Dan wasan tsakiya na Man City Ilkay Gundogan. POOL/AFP
Talla

Man City ta yi wa kyaftin din nata tayin wani sabon kwantiragin shekara guda, amma ya yi fatali da shi, kuma rahotanni na nuni da cewa Barcelona ta yi masa tayin kwantiragin shekaru 3 mai gwabi.

Kocin City, Pep Guardiola ya so ya ci gaba da zama da  Gundogan a kungiyar, duba da cewa yana daga cikin ‘yan wasan da suka taimaka ta lashe kofuna 3 a kakar da ta gabata.

Dan wasan tsakiyar na  tawagar kwallon kafar Jamus din ya buga wasanni 51 a kakar wasa ta 2022-2023, inda ya ci kwallaye 11.

Ya kuma buga wasa na tsawon mintuna 90 a wasan karshe na gasar zakarun nahiyar Turai, wasan da City ta doke Inter Milan da ci daya mai ban haushi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.