Isa ga babban shafi

Haaland na kokarin taimakawa Normay zuwa gasar Euro 2024

Dan wasan gaba na Manchester City Erling Haaland ya zura kwallaye biyu yayin da Norway ta samu nasara a gida kan Cyprus da ci 3 – 1 a wasan neman cancantar shiga gasar Euro 2024.

Dan wasan Norway Erling Haaland na murnar zira kwallon farko a wasan da kungiyar ta buga a wasan neman gurbi a gasar cin kofin nahiyar Turai na rukunin A tsakanin Norway da Scotland a filin wasa na Ullevaal da ke Olso, Norway, Asabar, 17 ga Yuni, 2023. (Heiko Junge/NTB Scanpix via AP)
Dan wasan Norway Erling Haaland na murnar zira kwallon farko a wasan da kungiyar ta buga a wasan neman gurbi a gasar cin kofin nahiyar Turai na rukunin A tsakanin Norway da Scotland a filin wasa na Ullevaal da ke Olso, Norway, Asabar, 17 ga Yuni, 2023. (Heiko Junge/NTB Scanpix via AP) AP - Heiko Junge
Talla

Ola Solbakken ne ya bude wa Norway cin kwallo daga shiga fili, kafin Haaland ya kara na biyu da na uku duk bayan dawowa daga hutu.

Yaci kwallo na biyun ne a bugun daga kai sai mai tsaron gida mintuna hudu tsakani da na farko, kafin Grigoris Kastanos ya rama daya ana dafa da tashi wasa.

Rashin karsashi

Norway dai ba ta samu gurbin shiga babbar gasa ba tun a gasar Euro 2000 kuma bata yi wani abin azo a gani a wannan wasannin na neman gurbi a yunkurin kaiwa ga gasar Euro 2024 mai zuwa a Jamus.

Sun yi rashin nasara da ci 3-0 a Spain, sun tashi kunnen doki 1-1 da Jojiya, suna doke Scotland a ranar Asabar amma a zura musu kwallaye biyu suka sha kashi da ci , 2-1.

Kokarin Haaland a City

Haaland ya ci wa City kwallaye 52 a dukkan gasa na kakar da aka karkare 2022-23, inda suka lashe Kofin Zakarun Turai da Premier da Kofin FA.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.