Isa ga babban shafi

Arsenal ta amince ta biya Fam miliyan 105 don dauko Declan Rice

Arsenal ta amince ta biya kudi har fam miliyan 105 don sayen dan wasan tsakiya na tawagar kwallon kafar Ingila da West Ham, Declan Rice.

Dan wasan tsakiya na West Ham, Declan Rice.
Dan wasan tsakiya na West Ham, Declan Rice. REUTERS - DAVID W CERNY
Talla

Ana dai ci gaba da tattaunawa  tsakanin Arsenal din da West Ham a kan yadda za a tsara cinikin dan wasan mai shekaru 24.

Wannan ciniki ya biyo bayan tayi na 3 da Arsenal din ta yi ne a kan dan wasan, bayan da a baya ta taya dan wasan sau biyu ana fatali da tayin, duba da cewa ba ta biya abin da ya kai faam miliyan 100 da kungiyar ta nema tun da farko baa.

Tun da farko, Manchester City, wadda aka yi fatali da taayin fam miliyan 90 da ta yi, ta janye daga takarar sayen dan wasan na tsakiya.

Kyaftin din na West Ham, Rice, ya kasance a kugiyar tun daga shekarar 2014, bayan zuwansa daga tawagar matasa ta Chelsea.

Kwantiraginsa da kungiyar kwallon kafa ta West Ham zai kare ne a shekarar 2024.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.