Isa ga babban shafi

Andre Onana: Manchester United ta kammala cinikin golan Inter Milan

Manchester United ta kammala siyan golan Inter Milan Andre Onana kan Yuro miliyan 55.

Andre Onana kenan a gasar zakarun Turai da tsohuwar kungiyarsa ta Inter Milan ta samu nasarar tsallakawa zagayen karshe.
Andre Onana kenan a gasar zakarun Turai da tsohuwar kungiyarsa ta Inter Milan ta samu nasarar tsallakawa zagayen karshe. REUTERS - ALBERTO LINGRIA
Talla

Dan wasan na Kamaru, mai shekaru 27, ya rattaba hannu kan kwantiragin shekaru biyar, tare da zabin tsawaita wa'adin watanni 12.

Tsohon mai tsaron ragar na Ajax na shirin haduwa da tawagar United a atisayen da suke yi na tunkarar kakar wasa ta bana a Amurka.

Onana zai maye gurbin David de Gea a matsayin mai tsaron gida ga United, bayan da dan kasar Sipaniya ya bar kungiyar a watan nan na Yuli yayin da kwantiraginsa ya kare bayan shekaru 12 a kungiyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.