Za'a kafa tarihi a gasar kofin duniya, idan 'Yar Morocco ta doka wasa da hijabi
A wannan Litinin aka dawo wasa na biyar a matakin rukuni na gasar neman cin kofin duniya na Mata da kasashen New Zealand da Australiya ke karban bakwanci.
Wallafawa ranar:
Italiya da Argentina ne suka bude wasa karfe bakwai na safe.
Tara da rabi akwai wasa tsakanin Jamus da Morocco, sai kuma wasa na uku a yau tsakanin Brazil da Panama.
Tarihi
Za'a iya fa kafa tarihi a rana ta biyar a gasar cin kofin duniya ta mata ta Fifan, muddun Nouhaila Benzina ‘Yar wasan Morocco ta taka leda a yau.
'Yar wasan bayan mai shekaru 25, za ta zama 'yar wasa ta farko da ta fara amfani da hijabi, a gasar cin kofin duniya a haduwar da za su yi da Jamus.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu