Isa ga babban shafi

New Zealand ta doke Norway a wasan farko na gasar cin kofin Duniyar Mata

Kasar New Zealand ta samu nasarar farko a gasar lashe kofin duniya ta mata da aka fara a Alhamis din nan, bayan da ta doke Norway da ta kwallo daya mai ban haushi a wasan da suka doka na farko a rukunin da su ke na A. 

Wasan New Zealand da Norway.
Wasan New Zealand da Norway. AP - Rick Rycroft
Talla

Hannah Wilkinson ce dai ta samu nasarar jefawa kasarta kwallo dayar da ta ba ta nasarar da ta dade ta na neman samu.   

A dayan wasan da aka buga tsakanin Australia da Ireland, Australia ce ta samu nasara da ci daya mai ban haushi a wasansu na rukunin B. 

Australia ta samu nasarar ce bayan da Steph Catley ta jefa mata kwallo a bugun daga kai sai mai tsaron gidan da ta samu a minti na 52 da fara wasa wato bayan dawowa daga hutun rabin lokaci. 

Wannan ne dai karon farko da kasashen biyu na New Zealand da Australia suka amshi bakoncin babbar gasar kwallon kafa ta mata a Duniya, kuma a wannan karon ne aka kara yawan kasashen da ke doka wannan gasa zuwa 32.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.