Isa ga babban shafi

Harbin bindiga ya yi sanadin mutuwar mutane a Auckland sa'o'i kafin gasar cin kofin duniya ta mata

Harbin dan bindiga dadi, ya yi sanadin mutuwar mutane biyu a tsakiyar birnin Auckland na kasar New Zealand, sa'o'i kadan kafin a fara bude gasar cin kofin duniya ta mata.

Filin wasa na Eden Park da ke birnin Auckland
Filin wasa na Eden Park da ke birnin Auckland © AFP - SAEED KHAN
Talla

Wasu mutane 6 da suka hada da jami’an ‘yan sanda sun samu raunuka sannan kuma dan bindigar ya mutu bayan faruwar lamarin da misalin karfe 07:22 na safiya(19:22 agogon GMT).

Firaministan kasar, Chris Hipkins, ya ce harin bashi da nasaba da ta’adddanci, saboda haka za a ci gaba da shirye-shiryen fara wannan gasa kamar yadda aka tsara.

Ya kara da cewa, tuni 'yan sanda suka yi shirin ko-ta-kwana kan duk wata barazana.

Har yanzu dai ba a gano dalilin siyasa ko akida na kai harin ba, in ji firaministan.

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, ta bayyana jajenta ga iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su, ta kuma ce tana tattaunawa da hukumomin New Zealand.

Za a bude gasar ne da wasa wasan farko tsakanin New Zealand da Norway a filin wasa na Eden Park da ke birnin Auckland.

Ministan wasanni Grant Robertson ya ce za a samu karin 'yan sanda, musamman wuraren da aka ware domin gudanar da wasanni, domin tabbatar da tsaro.

Kasashen New Zealand da Australia ne ke karbar bakuncin gasar cin kofin duniya ta mata karo na tara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.