Isa ga babban shafi
Canada 2015

Canada 2015 : Japan ta kai zagayen karshe

‘Yan matan Japan sun kai zagayen karshe a gasar cin kofin duniya ta Mata da ake gudanarwa a Canada bayan sun samu sa’a akan ‘yan matan Ingila ci 2 da 1. Ana dab da lokutan wasan ya cika ne ‘yar wasan Ingila Laura Bassett ta ci kansu, wanda ya ba Japan mai rike da kofin gasar nasara.

‘Yar wasan Ingila Laura Bassett ta ci kansu, wanda ya ba Japan mai rike da kofin gasar duniya na Mata nasara.
‘Yar wasan Ingila Laura Bassett ta ci kansu, wanda ya ba Japan mai rike da kofin gasar duniya na Mata nasara. REUTERS
Talla

Yanzu Japan za ta hadu ne da Amurka a wasan karshe a ranar Assabar inda zasu maimaita tarihin wasan karshe da suka fafata a 2011 a Frankfurt, da Japan ta samu nasara 3 da 1 a bugun fanariti,

‘Yan matan Ingila kuma yanzu za su hadu ne da ‘yan Matan Jamus a wasan neman na uku kafin buga wasan karshe a ranar Assabar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.