PSG za ta biya Mbappe euro miliyan 60 a matsayin tukwicin biyayya
Rahotanni daga birnin Paris na cewa akwai yiwuwar PSG za ta biya dan wasanta Kylian Mbappe kudaden da yawansu ya kai euro miliyan 60 a matsayin tukwicin yabawa da biyayya ko amintakar da ke tsakaninsu.
Wallafawa ranar:
Bayanan sun ce kungiyar ta París Saint Germaine za ta biya tauraron na ta makudan kudaden ne, muddin bai raba gari da ita har zuwa ranar 1 ga watan Agusta, duk da cewar dangantakar da ke tsakaninsu ta yi rauni matuka, biyo bayan kin tsawaita yarjejeniyarsa da yayi da ke shirin karewa a 2024.
Yanzu haka dai kungiyoyi da dama ne ke neman kulla yarjejeniya da dan wasan na Faransa.
Tuni kuma kungiyar Al-Hilal ta Saudiya ta gabatar da tayin euro miliyan 300 wanda PSG ta karba.
Sai dai Mbappe ya dage kan cigaba da zama a kungiyar ta sa, har zuwa lokacin da yarjejeniyarsa za ta kare.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu