Isa ga babban shafi

Switzerland ta fitar da New Zealand daga gasar cin kofin duniya ta Mata

Guda cikin kasashen da ke karbar bakoncin gasar cin kofin Duniya ta mata wato New Zealand ta fice daga gasar tun a matakin rukuni vayan wasa babu kwallo tsakaninta da Switzerlend a karawarsu ta safiyar yau lahadi.

'Yan wasan New Zealand.
'Yan wasan New Zealand. AFP - MARTY MELVILLE
Talla

Tashi wasan ba kwallo ya sanya New Zealand gaza karkarewa a sahun masu nasara na rukunin A kuma kasa ta farko mai karbar bakonci da ta taba ficewa daga gasar a tarihi.

Tun farko dai New Zealand ta faro wasanninta da gagarumar nasara inda ta zamo ta biyu a rukunin da ta ke, ko da ya ke Norway ta dawo samanta bayan ruwan kwallaye 6 da nema da ta yiwa Philippines.

Yayin wasan na yau, New Zealand ta hannun Jacqueline Hand ta yi kokarin zura kwallo don samun damar ci gaba da kasancewa a gasar amma kuma kwallon da aka tsammaci ta kai ga nasarar da bugu karfen raga tare da ficewa waje.

Ficewar New Zealand daga gasar ya bayar da matukar mamaki ganin yadda ta faro wasannin gasar da karsashi bayan doke Norway da kwallo 1 mai ban haushi a wasanta na farko.

Wannan ficewa ta New Zealand dai ba ta rasa nasaba da shan kayenta a hannun Philippines yayin wasansu na ranar talata a Wellington inda aka tashi wasa 1 da nema, kasar da ke matsayin mafi rashin karsashi a rukunin gasar na A.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.