Isa ga babban shafi

PSG na duba yiwuwar bayar da Mbappe a matsayin aro

Batun makomar dangantakar da ke kara yin rauni tsakanin PSG da tauraronta Kylian Mbappe na cigaba da daukar hankali, ganin yadda lamarin yaki ci yaki cinyewa.

Kylian Mbappé.
Kylian Mbappé. REUTERS - SARAH MEYSSONNIER
Talla

A yayin da Mbappe ya dage cewar sai ya karasa yarjejeniyarsa da kungiyar a shekarar 2024 ba tare da ya kara wa’adinta ba, majiyoyi kwarara sun bayyana cewar PSG ta fara Nazari kan yiwuwar aikewa da tauraron dan wasan na ta zuwa daya daga cikin kungiyoyin gasar Firmiyar Ingila a matsayin aro.

Wannan yunkuri na PSG  na zuwa ne a daidai lokacin da jaridun wasanni na duniya da dama suka ruwaito cewar, kungiyoyin Chelsea da Tottenham da ma wasu kari, sun gabatar da tayin neman sayen Mbappe ko dai da zunzurutun kudi ko kuma hade da mika wasu daga cikin ‘yan wasansu.

Babban abin damuwa ga kungiyar PSG a halin yanzu dai  shi ne rashin tabbas kan ko dan wasan na ta zai yadda ya koma wata  kungiya a matsayin aro domin karasa yarjejeniyar shekara guda da ta rage tsakaninsa da zakarun gasar League 1 na Faransa.

Idan har bukatar PSG ta tabbata, hakan na nufin nauyin cigaba da biyan Mbapppe albashin tsawon shekarar da ta rage ya sauka daga kanta, yayin da kuma dan wasan zai samu damar rabuwa da kungiyar a matsayin dan wasan da  babu wata yarjejeniya a kansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.