Tottenham ta yi fatali da tayin Bayern Munich a kan Kane
Tottenham ta sa kafa ta shure tayin baya bayan nan da Bayern Munich ta yi mata a kan dan wasan gabanta, kuma kyaftin din tawagar kwallon kafar Ingila, Harry Kane.
Wallafawa ranar:
Bayern ta yi fatan cewa za ta cimma yarjejeniya da Tottenham a kan wannan dan wasa, amma rahotanni na nuni da cewa bangarorin biyu sun gaza cimma matsaya a game da darajar dan wasan mai shekaru 30.
Bayern Munich din ta tsegunta cewa idan har sayen dan wasan gaban bai yiwu ba a wannan karon, za ta karkata hankalinta zuwa kan wasu ‘yan wasan.
Kane, wanda ya zura kwallaye 280 a raga daga wasanni 435 da ya buga wa Tottenham a dukkan gasa, shine ya jagoraanci kungiyar a fafatawarta da Shakhtar Donetsk a Lahadin da ta gabata a wasan share fagen shiga kaka mai zuwa.
Yanzu shekara da ya ce kawai ta rage kwantiragin dan wasan ya kare da Tottenham, kuma babu wata alama da ke nuni da cewa zai sabanta yarjejeniyar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu