Isa ga babban shafi

Barcelona da Chelsea ba su da tabbas kan kulla yarjejeniya da Neymar

Makomar Neymar idan har ya rabu da PSG na ci gaba da  kasancewa cikin rashin tabbas a dai dai lokkacin da dan wasan tare da kungiyar ta sa suka amince da Shirin rabuwar nan ba da jimawa ba.

Neymar da Silva Santos Júnior
Neymar da Silva Santos Júnior REUTERS - KIM HONG-JI
Talla

Sai dai mai yiwuwa burin kungiyoyin Barcelona da Chelsea wadanda ke saon kulla yarjejeniya da dan wasan ya gaza cika, saboda kalubalen da kowannensu ke fuskanta.

A bangaren Chelsea, a yayin da  ta kasance kungiyar da za fi dacewa da samun saukin sayen Neymar, ba lallai bane dan wasan ya amince da tayin komawa gare ta, la’akari da cewar ba samu tikitin buga gasar zakarun Turai ta bana ba.

Ita kuwa Barcelona da za a barje gumi da ita a gasar zakarun turan, b ata da kudin kulla yarjejeniya da dan wasan, sai dai fa idan har ya amince ya sauya sheka zuwa kungiyar Al Hilal da ke gasar kwallon kafar Saudiya, wadda majiyoyi ta ce a shirye ta ke ta mika wa Barcelona shi a matsayin aro, tsawon kakar wasa guda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.