Isa ga babban shafi

Chelsea ta sayi Caicedo a kan fam miliyan 100

Chelsea ta sayi dan wasan tsakiya na kungiyar kwallon kafa ta Brighton Moises Caicedo a kan kudi fam miliyan 100, wanda ka iya tashi zuwa faam miliyan 115.

 Moises Caicedo wanda Chelsea ta saya daga Brighton
Moises Caicedo wanda Chelsea ta saya daga Brighton AP - Kirsty Wigglesworth
Talla

A ranar Juma’a sai da Liverpool ta amince ta sayi dan wasan na tawagar kasar Ecuador mai shekaru 21 a kan fam miliyan 111, amma dan wasan ya fi son murza tamola  a Chelsea.

Caicedo, wanda a watan Fabrairun shekarar 2021 ya kkoma Brighton a kan kudi fam miliyan 4, ya rattaba hannu a kan kwantiragin shekaru 8 a Stamford Bridge.

Karin fam miliyan 15 da ake sa ran a yi  a kan farashin dan wasan, zai ta’allaka ne a kan yawan wasannin da zai buga wa Chelsea, kuma Brighton tana sa ran karbar wadannan kudade a cikin dan gajeren lokaci.

Idan Chelsea ta biya fam miliyan 115 a kan wannan dan wasa, hakan na nufin cewa sau biyu a wannan tana sayen ‘yan wasa  da irin kudin da ba taba kashewa a kungiyar ba, bayan da a watan Janairu ta sayi dan wasan tsakiya na tawagar Argentina, Enzo Fernandez.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.