Isa ga babban shafi

Ronaldo ya zama dan wasa mafi zura kwallo 3 a wasa guda da ake kira hat-trick

Dan wasan gaba na Portugal da ke taka leda da Al-Nassr ta Saudiya Cristiano Ronaldo ya kafa tarihin zura kwallaye 3 a wasa guda da ake kira da hat-trick a turance har sau 63 a tsawon lokacin da ya shafe ya na taka leda a fagen tamaula.

Cristiano Ronaldo na Portugal bayan nasarar zura kwallaye 3 a wasan da Al-Nassr ta lallasa Al Fateh da kwallaye 5 da nema.
Cristiano Ronaldo na Portugal bayan nasarar zura kwallaye 3 a wasan da Al-Nassr ta lallasa Al Fateh da kwallaye 5 da nema. © AFP - ALI AL-HAJI
Talla

Wannan nasara ta bai wa zakaran na Portugal damar shiga gaban kowanne dan wasan a yawan zura kwallayen na Hat-tricks ko kuma kwallo 3 a wasa guda.

Ronaldo mai shekaru 38 ya kafa wannan tarihin ne bayan nasarar sa ta zura kwallaye kwallaye har 3 a ragar Al Fateh ranar juma’ar da ta gabata, wanda ya zama karon farko da ya ke irin wannan nasara ta zura kwallo 3 a wasa guda tun bayan komawarsa Al-Nassr.

Yayin wasan wanda aka tashi kwallo 5 da nema, Sadio Mane ne ya zura sauran kwallayen biyu da ya baiwa Al-Nassr gagarumar nasara.

A baya-bayan nan ne Sadio Mane ya koma Al-Nassr ta Saudiya daga Bayern Munich ta Jamus.
A baya-bayan nan ne Sadio Mane ya koma Al-Nassr ta Saudiya daga Bayern Munich ta Jamus. AFP - ALI ALHAJI

Yanzu haka dai Ronaldo na Al-Nassr shi ke matsayin mafi yawan zura kwallayen 3 a wasa guda, wadda ya yi nasarar zurawa har sau 63 biye da takwaransa Lionel Messi na Inter Miami mai 57 ka na Robert Lewandowski da 30 sai kuma Luis Suarez da 29.

Sauran ‘yan wasan da suka yi nasarar zura kwallaye 3 a wasa guda sun hada da Mario Gomez sai 18 kana Sergio Aguero da 18 sai kuma Erling Haaland sai 18 sannan Zlatan Ibrahim sau 17 sannan Harry Kane da 15 Kylian Mbappe sau 14.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.