Isa ga babban shafi

Arsenal ta doke City a gasar Premier, karon farko tun shekarar 2015

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta doke zakarar gasar Premier Ingila a kakar da ta gabata Manchester City, da ci da mai ban haushi, a wasansu na farko na gasar a wannan kaka.

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Arsenal Gabriel Martinelli, yayin murnar kwallon da ya zura a ragar Man City.
Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Arsenal Gabriel Martinelli, yayin murnar kwallon da ya zura a ragar Man City. REUTERS - DAVID KLEIN
Talla

Karon farko ke nan da Arsenal ta doke Manchester City a gasar Premier tun shekarar 2015, bayan kwallon da Gabriel Martinelli ya zura a minti na 86 a filin wasa na Emirates a yau Lahadi.

Wannan nasarar da Arsenal ta samu ta bata damar komawa matsayi na biyu a teburin gasar, duk da dai makinsu daya da Tottenham da ke jagorantar teburin gasar bayan wasannin mako na 8 da maki 20.

Mai horas da kungiyar Manchester City Pep Guardiola bayan tashi daga wasan, ya ce dama haka wasa ya gada, sun samu ta su damar amma basu jefa kwallo ba, ya yin da Arsenal ta yi amfani da ta ta damar wajen samun nasara.

A baya-bayannan, wannan ne karo na farko da kungiyar Manchester City ta yi nasara a hannun wata kungiya a wasanni biyu a jere, domin a wasan karshe da suka yi a kofin Community Shield, Arsenal ce ta yi nasara kan City a bugun daga kai sai mai tsaron gida bayan tashi wasan daya da daya.  

Arsenal ta kara samun kwarin gwiwa a kokarinta na ganin ta lashe gasar a wannan kaka, ganin yadda a kakar da ta gabata ita ce ta kare a mataki na biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.