Isa ga babban shafi

Paulo Dybala zai yi jinyar mako 4 dai dai lokacin da Roma ke fama da koma baya

Kungiyar kwallon kafa ta Roma ta tabbatar da cewa dan wasanta na gaba Paulo Dybala zai shafe fiye da wata guda ya na jinyar raunin da ya samu a wasan da suka yi nasara kan Cagliari da kwallaye 4 da1.

Daga Juventus ne Paulo Dybala ya koma Roma da taka leda.
Daga Juventus ne Paulo Dybala ya koma Roma da taka leda. © REUTERS/Massimo Pinca
Talla

Tauraron na Argentina ya bar fili ranar Lahadi cikin kwalla bayan da jita-jita ke bayyana yiwuwar ya kare ilahirin sauran watannin shekarar nan ya na jinyar raunin.

Dybala wanda ya koma Roma daga Juventus ya samu raunin ne bayan wata muguwar haduwa da suka yi da mai tsaron baya Matteo

Sanarwar da Roma ta fitar ta ce dan wasan na ta ya samu rauni ne a gwiwa kuma zai shafe makwanni 4 ya na jinya.

Wannan na nuna cewa Dybala zai rasa damar bulaguro da tawagar ta Roma zuwa Inter Milan a wasansu na ranar 29 ga watan da muke ciki na Oktoba haka zalika haduwar su da Lazio ta watan Nuwamba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.