Isa ga babban shafi

Bukayo Saka zai shafe lokaci ya na jinyar raunin da ya samu- Ingila

Hukumar kwallon kafar Ingila ta tabbatar da cewa Bukayo Saka ba zai samu damar take leda a wasan da kasar za ta kara da Australia ranar 13 ga watan Oktoban nan ba, haka zalika haduwarta da Italiya a ranar 17 ga watan karkashin wasan neman gurbi a gasar cikin kofin nahiyar Turai.

Bukayo Saka yayin murnar zura kwallo a wasan Ingila.
Bukayo Saka yayin murnar zura kwallo a wasan Ingila. © AFP - ADRIAN DENNIS
Talla

Saka wanda bai taka leda a wasan da Arsenal ta doke Manchester City da kwallo 1 mai ban haushi a gasar Firimiyar Ingila ba, sakamakon raunin da ya samu a cinya, hukumar kwallon kafar Ingila ta ce duk da cewa bazai samu damar taka leda a wasannin biyu ba, amma kai tsaye baza a cire sunanshi daga zubin ‘yan wasa 26 da kasar ta ware ba.

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal Mikel Arteta ya bayyana cewa dan wasan sam ba zai iya taka leda a wasannin nan kusa ba, lura da yadda yak e bukatar lokacin don jinyar raunin nasa.

Wasan na Arsenal a ranar Lahadin da ta gabata, shi ne karon farko da dan wasan mai shekaru 22 bai samu damar dokawa ba a baya-bayan nan inda aka ga haskawarsa a wasanni 87 karkashin jagorancin Arteta.

Dan wasan na Ingila ya yi famin rauni ne a karawar da Arsenal ta yi rashin nasara a hannun Lens da kwallaye 2 da 1 karkashin wasannin cin kofin zakarun Turai.

A cewar Arteta Saka zai dauki lokaci ya na jinya ganain iya dawowa fili, domin yanzu haka ko atisaye baya iya yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.