Isa ga babban shafi

Tottenham ta amince da farashin Bayern Munich kan Harry Kane

Kungiyoyin kwallon kafa na Bayern Munich da Tottenham sun amince da cimma yarjejeniya kan cinikin kyaftin din tawagar mai doka firimiyar Ingila Harry Kane wanda kudinsa ya kai yuro miliyan 100 dai dai da fam  miliyan 86 da rabi.

Da yiwuwar a kammala cinikin na Harry Kane kowanne lokaci daga yanzu bayan amincewar bangarorin biyu.
Da yiwuwar a kammala cinikin na Harry Kane kowanne lokaci daga yanzu bayan amincewar bangarorin biyu. REUTERS - DAVID KLEIN
Talla

Kane mai shekaru 30 wanda ke da sauran shekara guda a kwantiraginsa da Tottenham yanzu bangarorin biyu sun damka masa wuka da nama domin kuwa shi ke da tacewa a cinikin walau dai ya amince da komawa gasar ta Bundesliga ko kuma ya kammala kwantiragin nasa wanda haka Tottenham ta ke fata.

Dan wasan gaban wanda ke matsayin mafi zura kwallo a tarihin Tottenham ya doka mata wasanni 435 tare da zura kwallaye 280.

Tsawon lokaci Kane ya shafe yana son sauya sheka zuwa wata kungiya ta daban bayan shawarwarin masana game da rashin tasirin kungiyar tasa gareshi lura da yadda ya shafe tsawon lokaci ba tare da nasarar kafa wani tarihi ba.

Sai dai kuma bayan rushewar yunkurin cinikinsa a lokuta da dama, cikin wannan kaka Manchester United ta fara nuna sha’awar sayenshi gabanin Bayern Munich ta mayar da shi lamba daya a sahun ‘yan wasan da ta ke fatan saya a wannan kaka.

Kafin Bayern Munich din Real Madrid na sahun kungiyoyin da ke harin Kane amma kuma bayan matakin Mbappe na shirin raba gari da PSG ana ganin dalilin ya sanya Madrid janyewa don komawa ga matashin dan wasan wanda ta jima ta na maitar saye.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.