Isa ga babban shafi

Harin dan bindiga ya tilasta dakatar da wasan Belgium da Sweden

An dakatar da wasan neman tikitin buga gasar cin kofin kasashen nahiyar Turai tsakanin Belgium da Sweden saboda dalillai na tsaro, bayan da wani dan bindiga ya  harbe mutane biyu har lahira a birnin Brussels.

Masu kallo bayan dakatar da wasan Sweden da Belgium a filin wasa na Sarki Baudouin da ke birnin Brussels. 16 ga Oktoba, 2023.
Masu kallo bayan dakatar da wasan Sweden da Belgium a filin wasa na Sarki Baudouin da ke birnin Brussels. 16 ga Oktoba, 2023. REUTERS - YVES HERMAN
Talla

Tawagar ‘yan wasan Sweden ce ta nemi hukumar kwallon kafar Turai UEFA ta dakatar da wasan da suke bugawa a ranar Litinin, bayan da suka tafi hutun rabin lokaci.

Bayanai sun ce an aikata kisan gillar ne kafin fara wasan, to amma tilas aka dakatar da fafatawar yayin da ake 1-1, saboda tserewar da dan bindigar yayi, bayan kashe mutane biyu dukkaninsu ‘yan Sweden, wanda jami’an tsaro ke ci gaba da farautarsa.

Babu dai karin bayani kan ko mutanen da aka kashe sun zo Brussels ne domin kalllon wasan neman cancantar da kasarsu za ta kara da Belgium.

Wani lokaci nan gaba ake sa ran hukumar UEFA ta fayyace makomar wasan na Belgium da Sweden.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.