A karon farko cikin shekaru 46 Ingila ta samu nasara kan Italiya a gida
Ingila ta samu tikitin halartar gasar cin kofin kasashen Turai ta 2024, bayan lallasa Italiya da kwallaye 3-1 a filin was ana Wembley da ke birnin London, yayin fafatwar da suka yi a ranar Talata.
Wallafawa ranar:
Tawagar kwallon kafar ta Ingila ta samu nasarar ce ta hannun ‘yan wasanta Harry Kane da mai kwallaye biyu da kuma Marcus Rashford da jefa guda.
Kafin wasan dai, maki guda daya, Ingilar ke bukata domin kai wa gasar ta Euro da Jamus za ta karbi bakunci, amma daga bisani ta samu gagarumar nasarar, duk da cewar ita aka fara zura wa kwallo a raga ta hannun dan wasan Italiya Gianluca Scamacca.
Karo na farko kenan da Ingila ta samu nasara kan Italiya a gida, tun bayan watan Nuwamban shekarar 1977.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu