Isa ga babban shafi
AFCON

Nasarar Super Eagles ce tafi muhimmanci akan tawa - Osimhen

Dan wasan gaba na tawagar Super Eagels Victor Osimhen, ya ce babu wani matsin lambar da ya ke fuskanta, don ganin tauraruwarsa ta haske a gasar lashe kofin Afrika AFCON da ke gudana a Ivory Coast.

Dan wasan gaba na tawagar Super Eagles Victor Osimhen.
Dan wasan gaba na tawagar Super Eagles Victor Osimhen. © rfi fulfulde
Talla

Dan wasan mai shekaru 25 da ke takawa kungiyar Napoli leda, kwallo daya ya zura a raga a wasanni biyu da ya buga a gasar.

Wasu da dama na dora alhakin rashin zura kwallayen da dan wasan bayyi ba kan matsin lambar da ya ke fuskanta, ganin shi ke rike da kambun kyautar gwarzon dan kwallon Afrika.

Lokoacin da dan wasan gaba na Super Eagles Victor Osimhen ya zura kwallonsa a ragar Equatorial Guinea, a karawar da suka tashi kunnen doki, 1-1.
Lokoacin da dan wasan gaba na Super Eagles Victor Osimhen ya zura kwallonsa a ragar Equatorial Guinea, a karawar da suka tashi kunnen doki, 1-1. AP - Sunday Alamba

 

Toh sai dai dan wasan ya ce abun ba haka ya ke ba, domin a cewarsa ya maida hankali ne wajen samun nasarar tawagarsa ta Super Eagles a Cote d’Ivoire.

 

“Abin da ya fi muhimmanci gare ni a yanzu shi ne muyi nasara tare da tawagata, in tabbatar da cewa tawagar ta yi nasara da kuma lashe AFCON.

“Ban damu da yin nasara ta ni kadai ba, zan iya kasancewa a benci yayinda sauran 'yan wasan su buga don samar mana nasara. "

A gobe Litinin ne dai tawagar Super Eagles za ta kammala wasanninta na rukuni, da karawa tsakaninta da Guinea-Bissau a filin wasan na Felix Houphouet Boigny da ke birnin Abidjan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.