Isa ga babban shafi
AFCON

Wasu daga cikin muhimman abubuwan da suka faru a wasannin farko na gasar AFCON

A jiya laraba ne aka kammala dukkanin wasan farko a matakin rukuni na gasar lashe kofin Afrika.

Wasu daga cikin abubuwan da suka faru a wasannin farko na gasar lashe kofin Afrika AFCON.
Wasu daga cikin abubuwan da suka faru a wasannin farko na gasar lashe kofin Afrika AFCON. REUTERS - THAIER AL-SUDANI
Talla

Akwai abubuwa da dama da suka dauki hankalin jama’a game da yadda wasannin farkon suka gudana.

Yawan kwallayen da aka jefa

Bayan guda wasanni 12 da tawagar kasashe 24 suka yi a gasar AFCON karo na 34 da ke gudana Ivory Coast, kwallaye 27 ne kadai aka samu nasarar jefawa a raga.

Ganin yadda aka samu karancin jefa kwallaye a raga, masu bibiyar harkar wasanni ganin cewar gasar ta bana akwai sauyi a cikinta, musamman yadda a baya manyan kasashen da suka mamaye kwallon kafar nahiyar ke yiwa kananan kasashe ruwan kwallaye.

Haka nan, sabanin baya da ake samun mutane na jefa kwallaye da dama a raga, a wannan karon dai-daikun mutane ne suka jefa dukkanin kwallayen in banda Lamine Camara, dan wasan Senegal da ya samu nasarar jefa kwallo biyu a raga.

Yawan masu kwallon gasar a fili

 

Yadda wasu daga cikin filayen wasanni ke kasancewa babu muta ne sosai, a gasar lashe kofin Afrika AFCON da ke gudana a Ivory Coast.
Yadda wasu daga cikin filayen wasanni ke kasancewa babu muta ne sosai, a gasar lashe kofin Afrika AFCON da ke gudana a Ivory Coast. © Daily Trust

Wani abu da ya dauki hankalin jama’a shi ne yadda aka samu karancin masu shiga kallon wasannin gasar, domin alkaluman da hukumomi suka fitar, sun nuna cewa mutane dubu dari da 66 da dari 924 ne suka shiga filin wasa don kallon wasanni 12 da aka buga.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.