Isa ga babban shafi

Madrid ta yi watsi da zargin tirsasawa alkalan wasan La Liga

La Liga – Kungiyar Real Madrid ta yi watsi da zargin Barcelona cewar ta na tasiri a kan rawar da alkalan wasa ke yi wajen busa wasannin La Liga, inda ta bayyana zargin a matsayin mara tushe.

Carlo Ancelotti da 'dan wasan sa Vinicius Jnr
Carlo Ancelotti da 'dan wasan sa Vinicius Jnr AP - Jose Breton
Talla

Mai horar da ‘yan wasan Madrid Carlos Ancelotti ya bayyana zargin na Barcelona a matsayin mara inganci wanda kuma ke tattare da rashin kwarewa daga bangaren Barcelonan.

Ancelotti yace a matsayin sa na kwararre ba zai taba durkusar da kan sa ba wajen yin irin wannan zargi da kuma neman batawa gasar La Liga suna.

Manajan ya roki manema labarai da kar su sake tambayarsa a kan wannan zargin, domin baya bukatar yin magana a kai.

Shugaban kungiyar Barcelona Joan Laporta da manajan kungiyar Xavi Hernandez sun gabatar da korafi a kan yadda tashar talabijin din Madrid ke nuna rahotan dake sukar alkalan wasan.

Xavi ya kuma bayyana cewar an gurbata harkar alkalanci a La Liga saboda yadda shugabannin Madrid ke tirsasawa alkalan wasa.

Yanzu haka akwai tazarar maki 10 tsakanin Real Madrid da Barcelona a teburin La Liga, yayin da kungiyar ke shirin karawa da Atletico Madrid a karshen wannan mako.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.