Isa ga babban shafi
Fadar Vatican

Jorge Mario Bergoglio ne sabon Fafaroma, wanda zai amsa sunan Fafaroma Francis

An zabi Jorge Mario Bergoglio, a matsayin sabon Fafaroma, zai kuma amsa sunan Fafaroma Francis wanda dan asalin kasar Argentina, a matsayin Fafaroma na farko da ya fito daga wata Nahiya ba Nahiyar Turai ba.

Sabon Fafaroma Francis
Sabon Fafaroma Francis
Talla

Tun a yammacin Laraba ne, rahotanni daga Fadar Vatican suka nuna cewa farin hayaki ya bayyana a fadar, wanda hakan alamu ne da ke nuna cewa an yi dacenzaben sabon Fafaroma, wanda shi zai shugabanci mabiya darikar Katolika a duniya.

Hayakin ya bayyana ne da yammacin Laraba bayan manyan Limamai sun kada kuri’unsu a karo na biyar a cikin kwanaki biyu.

Da bayyanar hayakin ne kuma karaurawa suka fara kadawa a farfajiyar St. Peter, da ke fadar ta Vatican.

Fafaroma Benedict na goma sha biyu  ya yi murabus ne a ranar 28 ga watan Febrairu inda ya ba da uzurin yawan shekaru da ya ke fama da su wanda hakan kuma ya bar gibi a fadar ta Vatican.

A ranar Talata ne manyan Limaman fadar ta Vatican suka shiga shirye-shiryen fara zaben wanda zai maye gurbin Fafaroma Benedict da mai murabus.

An dai ga dubban mutane sun yi dafifi a  dandalin St. Peter suna dakon fitowar farin hayakin, a yayin da ake ta tafka ruwan sama kamar da bakin kwarya, a dai dai lokacin da Limamai 115 suke gudanar da zaben.

A lokacin zaben Fafaroma Benedict da ya yi murabus, wanda kuma ya gaji Fafaroma John Paul na Biyu, an gudanar da zaben har zuwa karo na hudu sabanin karo na biyar  a wannan lokaci ba.

A dai dai lokacin hada wannan rahoto ana dakon fitowar sabon Fafaroma wanda za a bayyana shi kamin ya bayyana ga jama'a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.