Isa ga babban shafi
Kwallon kafa

Ferdinand ya fice daga cikin ‘Yan wasan Ingila

A yayin da ake shirin fara karawa a fagen wasannin share fagen gasar cin kofin duniya a kasar Brazil a shekara mai zuwa, dan wasan kasar Ingila, har ila yau mai tsaron gidan Manchester United, Rio Ferdinand ba zai samu damar buga wasan da Ingilan za ta yi da San Marino a ranar Juma’ar nan mai zuwa ba.

Dan wasan Manchester United Rio Ferdinand
Dan wasan Manchester United Rio Ferdinand REUTERS/Nigel Roddis
Talla

Rahotannin na nuna cewa Ferdinand, dan shekaru 34 ba zai buga wasan ba ne saboda dalilin da ya shafi rashin lafiya, koda yake rahotanni basu bayyana asalin abin da yake damun Ferdinand ba.

Rabon da Ferdinand ya buga kwallo a matakin kasarsa ta Ingila, tun a watan Yunin shekarar 2011 a lokacin da suka kara da kasar Switzerland inda aka tashi a wasan da kunnen doki, wato da ci 2-2.

Ana sa ran za a maye gurbin Feridnand da dan wasan Tottenham, Steven Caulker.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.