Za a mika Ntaganda ga Kotun Hague a wannan makon
Mai Gabatar da kara na kotun hukunta manyan laifufuka, Fatou Bensouda, ta ce a cikin wannan mako ake sa ran kai Janar Bosco Ntaganda, shugaban ‘Yan tawayen Jamhuriyar Demokradiyar Congo birnin Haque, dan fuskantar shari’a.
Wallafawa ranar:
Idan dai ba’a manta ba, Janar Ntaganda ya mika kansa ga Ofishin Jakadancin Amurka a Rwanda, kuma yana daga cikin wadanda kotun ke nema ruwa a jallo, saboda zargin kashe jama’a da kuma sanya yara kanana cikin yaki.
A yanzu haka kasar ta Rwanda na ta nisanta kanta da Ntaganda inda Ministan Shari’ar kasar, Tharsis Karugarama, ya ce bazai yin magani da yawun Ntaganda ba, sai y ace ya kamata a bashi dama ya kare kansa bisa zargin da ake yi mai.
“Ba zan iya magana da yawun Janar Ntaganda ba, ya yi zabi, shi Janar ne na sojin Congo a baya, ya zabi mika kansa dan kai shi kotun duniya, saboda haka ya dace a bashi dama dan fuskantar kotun domin kare kansa.” Inji Minista Karugarama.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu