Isa ga babban shafi
Bankin Duniya

Shirin yaki da talauci a Duniya

Bankin Duniya ya kaddamar da sabon yunkurin yaki da matsanancin talauci, inda zai fadada aikinsa a kasashen da ke fama da tashe-tashen hankula.Shirin bankin Duniyar na tsawon shekaru biyar, zai mayar da hankali kan kasashen da ke fama da bakin talauci ko kuma matsakaici da kuma kasashen da ke fuskantar matsalar kwarrarar ‘yan gudun hijira.

Takardun kudin  na kasashen Duniya
Takardun kudin na kasashen Duniya Getty Images/Rubberball/Mike Kemp
Talla

Kididdigar masana tattalin arziki na kasa da kasa, ta nuna cewa adadin mutanen da ke fama da matsanancin talauci a nahiyar Afrika ya kai matakin ha’ula’i.

Masanan sun kara da cewa, matsalar za ta ci gaba da tsananta, saboda saurin karuwar yawan al’umma da nahiyar za ta fuskanta a shekaru 10 da ke tafe.

Yayin wata ganawa da kamfanin dillancin labarai na AFP, shugaban bankin duniya ya ce kalubalen da ke fuskantar nahiyar ta Afrika ba karami bane, dan haka akwai bukatar ware kudade masu yawan gaske da kuma tsara hanyoyin samar da guraben ayyukan yi, da kuma ababen more rayuwa, domin tafiya dai dai da karuwar yawan al’umma a Afrika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.