Isa ga babban shafi
Turai

Manyan dabbobin ruwa na whales 380 ne suka mutu a yammacin Australia

Akalla manyan dabbobin ruwa na whales 380 ne suka mutu sakamakon kafewar ruwa a yammacin Australia, kamar yadda hukumomi suka sanar yau Laraba, yayin da aka yanke kaunar ceto da dama da ke cikin mawuyacin hali.

Manyan  dabbobin ruwa na whales a yammacin Australia
Manyan dabbobin ruwa na whales a yammacin Australia AFP
Talla

Kusan ilahirin wadannan halittun ruwa na whales, masu dogayen filafilai guda 460 da suka yi makuwa a tashar jirgin ruwa na Macquarie Habour, a tsibirin da ke yammacin jihar Tasmania ta Australian sun salwanta.

An yi amannar cewa wannan ce makuwa mafi girma na irin wadannan halittu da aka taba samu a Australia, kuma tana cikin daidaiku da suka taba faruwa a duniya.

A ranar Litinin aka gano jerin farko na wadannan manyan halittun cikin teku su na fama a inda ruwa yayi karanci, lamarin da ya sa hukumomi kokarin ceto su daga shurin yashi da rairayin bakin teku a inda kananan jiragen ruwa ne kawai ke iya zuwa.

Wata tawagar ceto mai kunshe da masu kwarewa da kiyaye halittu, da kwararrun masu aikin sa kai da masu kiwon kifi sun shafe tsawon kwanaki suna kutsawa cikin ruwan kankara don ceto wadannan halittu na whales, wadanda tsawonsu zai iya kai kafa 20 ko mita 6, nauyinsu kuma tan daya kowanne, kuma sun yi nasarar ceto da dama a jiya Talata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.