Isa ga babban shafi
Turai-Tsananin zafi

Tsananin zafi a sassan Turai ya fara kashe kifayen da ke ruwa

Tsananin zafin da ake ci gaba da fuskanta a kasashen Turai ya yi sanadiyyar mutuwar dubban kifin da ke gabar ruwan kasar Switzerland.Baya ga tarin kifayen da tsananin zafin ke yiwa illa akwai kuma dubban jama'a da yanzu haka ake amfani da manyan motoci don yi musu feshin ruwa don sama musu saukin rayuwa.

Yanzu haka dai dubban mutane ne a sassan nahiyar ta Turai suka mayar da bakin ruwa wajen zamansu na din-din-din don samun sauki daga tsananin zafin da su ke fuskanta.
Yanzu haka dai dubban mutane ne a sassan nahiyar ta Turai suka mayar da bakin ruwa wajen zamansu na din-din-din don samun sauki daga tsananin zafin da su ke fuskanta. REUTERS/Heino Kalis
Talla

Rahotanni sun ce Yankunan da aka samu mutuwar kifin sun hada da kogin Rhine da ke tafiya zuwa tafkin Constance da mashigin ruwan Rhine, inda aka samu tarin kifin sun taso saman ruwan bayan mutuwar su.

Andreas Vogeli, jami’in hukumar da ke kula da ma’aikatun gona, ya ce sun kwashe kwanaki suna kallon matattun kifin na yawo a saman ruwa.

Tun a makwannin da suka gabata ne, hukumomi a kasashen na Turai da tsananin zafin ya ta'azzara suka yi umarnin kulle duk wasu guraren gashi don samar da sauki ga al'umma.

Haka zalika a bangare guda dubban mutane a nahiyar ta Turai sun mayar da bakin ruwa wajen zamansu na din-din-din don samun sauki daga tsananin zafin da ke kara ta'azzara.

Ana dai ganin tsananin zabin ya samo asali ne daga gobarar dajin da wasu kasashen na Turai suka fuskanta a baya-bayan nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.