Shugabar Liberia mai barin gado, Ellen Johnson Sirleaf ta bukaci al’ummar kasar da su mutunta sakamakon zaben da zai kawo karshen mulkinta na shekaru 12. A wani gajeren jawabin da ta yi wa 'yan kasar yammacin jiya, shugabar ta bukace su da su gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali da kuma mutunta sakamakonsa. Sirleaf ta ce a karo na uku a tarihin kasar suna kokarin ganin an mika wa zababben shugaban kasa mulki ba tare da samun matsala ba. Dangane, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dr. Kole Shettima na Mc Authur Foundation.
Sauran kashi-kashi
-
Munyi mamakin yadda Amurka ta san bayanan sirrin tsaron mu - Raɗɗa
Wasu gwamnonin arewacin Najeriya 10 da ke fuskantar matsalolin tsaro, sun kammala taron da suka je Amurka kan matsalar da kuma hanyoyin samar da zaman lafiya.26/04/202405:17 -
Bashir Dan-Malam kan karancin man fetur a sassan Najeriya
Rahotanni daga sassan arewacin Najeriya na nuna cewar an fara samun karancin mai a gidajen mai, abinda ya sa wasu masu man suka kara farashin da suke sayar da kowacce lita.25/04/202403:16 -
Arewa maso Yammacin Najeriya ne mafi hatsari saboda matsalar tsaro - Bincike
Kungiyar 'Global Rights' ta bayyana yankin arewa maso yammacin Najeriya a matsayin mafi hadari, saboda yadda 'yan bindiga ke kisa da take hakkin Bil Adama ba tare da kaukautawa ba.18/04/202403:16 -
Kuskure ne a yi tunanin ɗagawar darajar naira ba zai ɗore ba - Dakta Kurfi
Darajar Naira na cigaba da ɗagawa a Najeriya tare da saukar farashin wasu kayayyakin abinci a wasu kasuwannin ƙasar, abinda ya sa wasu tunanin cewar tasirin saukar Dalar ne ya sanya wasu kayayyakin suka fara sauka.17/04/202403:19 -
Tattaunawa da Sanata Ikira Aliyu Bilbis kan tsaro a jihar Zamfara
Hukumomi a Najeriya daga matakin jiha zuwa na kasar baki ɗaya na daukar matakai daban daban wajen samar da zaman lafiya a jihar Zamfara, amma har ya zuwa wannan lokaci ba'a kai ga cimma biyan bukata ba.16/04/202403:26