Dakarun Iraki sun kama garuruwa a yankin kirkuk mai neman ballewa...
Dakarun Iraki sun karbe ikon wasu kauyuka daga hanun kurdawa a yankin Kirkuk, bayan tafka wani gumurzu da suka yi, a yayin da Amruka ta yi kiran a maida wukaikai kube.
Wallafawa ranar:
Rahotanni sun ce, dakarun rundunar hadaka ta JOC da ta hada daukacin jami’an tsaron Iraki ne, a jiya juma’a ta sanar da kwace garin 'Altun Kupri", da ya hada kauyuka 36 a maraba’in Km 530 inda kimanin kabilun Kurdawa da Turkmen dubu 56 ke rayuwa
Kasar Amruka ta bayyana damuwarta da sabon tashin hankalin dake faruwa a arewacin kasar ta Iraki. Kafin ta bukaci Sojan Iraki su takaita kai kawonsu a yankin na Kirkuk
Wannan sabon tashin hankali dai na zuwa ne kasa da wata guda bayan kada kuri’ar tabbatar da samun cikaken yanci cin gashin kan yankin kurdawan daga kasar ta Iraki
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu