rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Majalisar Dinkin Duniya Indonesia

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Girgizar kasa zata shafi al'ummar Indonesia miliyan 47 - Hasashe

media
Wasu 'yan Indonesia, yayinda suke kokarin neman kayayyakin da zasu iya dauka daga karkashin ginin da ya rushe, sakamakon girgizar kasa da ta afkawa yankin Pidie Jaya, da ke lardin Aceh, na kasar Indonesia. 10 ga Disamba, 2016. REUTERS/Darren Whiteside

Majalisar Dinkin Duniya ta yi hasashen cewa, idan girgizar kasa ta sake afkawa Indonesia, mutane dubu goma ne zasu hallaka cikin awanni 24, yayin da zata shafi wasu kimanin miliyan 47.


Hasashen na kunshe ne cikin wani jadawali da Majalisar ta tsara, na daukar matakan agajin gaggawa a duk lokacin da girgizar kasa ta sake afkawa kasar ta Indonesia.

Majalisar Dinkin Duniyar ta kafa ginshikin hasashen nata ne, ta hanyar kwatanta irin barnar da girgizar kasa mai karfin maki 7.8 ta yi a yankin Sunda da ke tsakanin tsibiran Java da Sumatra na kasar ta Indonesia.

Hasashen ya ce bayaga mutane Dubu 10 da zasu iya rasa rayukansu sakamakon girgizar kasar da ka iya aukuwa nan gaba, akalla mutane dubu 60 ne zasu shiga cikin munin yanayi na jikkata, wasu dubu dari biyu, zasu samu kananan raunuka, yayinda mutane miliyan 9 da dubu 600 zasu rasa muhallansu.

Bayanin hasashen da ya kara haifar da fargaba shi ne akwai yiwuwar, daga cikin mutane miliyan biyu da dubu dari biyar, da zasu bukaci agajin gaggawa, za’a samu damar taimakawa kasa da mutane 2 ne kawai, daga cikin 10 da zasu bukaci hakan, zalika za’a rasa wutar lantarki, da layin tarho a sassan kasar ta Indonesia na tsawon akalla makwanni biyu, sai kuma muhalli da zai gurbata sakamakon kwaranyar sinadarai da kuma danyen mai.

Lamarin da zai haifar da tsaikon mako guda na rarraba manfetur zuwa sassan kasar, bayaga durkusar da ayyukan tashoshin jiragen sama da na ruwa.

A shekarar 2004, kakkkarfar girgizar kasar tsunami da ta faro daga tekun India, ta hallaka mutane dubu dari biyu da ashirin da shida, a cikin kasashe sha uku da ta ratsa, kuma sama da dubu shabiyu sun hallaka ne Indonesia.

Tun daga lokacin ne kuma aka dauki matakai na kafa cibiyoyin bincike da suke hasashen aukuwar makamancin wannan Iftila’in.