rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Faransa Jamus Bakin-haure Tarayyar Turai

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Faransa da Jamus za su magance kwararar baki a Turai

media
Wasu daga cikin bakin hauren da ke neman maaka a kasashen Turai Hermine Poschmann/Misson-Lifeline/Handout via REUTERS

Kasashen Faransa da Jamus sun bukaci lalubo wata sabuwar hanyar magance matsalar kwararar bakin haure zuwa Turai bayan rashin fahimtar juna a tsakaninsu ta jefa daruruwan bakin cikin wani hali, in da suke yawo kan teku ba tare da samu mafaka ba.


Shugabannin kasashe 16 daga cikin 28 na Turai suka gudanar da wani taron gaggawa a Brussels domin shawo kan matsalar wajen ganin kasar ta karbi bakin da suka isa gabar-ruwan Italiya da kuma wasu kasashen Turai.

Tuni kasar Italiya ta kekashe kasa cewar, ba zata sake karbar bakin da suka isa kasarta ba, kamar yadda sabuwar gwamnatin da ke adawa da karbar bakin ta bayyana.

Wannan ya jefa rayuwar baki 239 da ke cikin kwale-kwalen da ya fito daga Afrika cikin hadari, cikinsu har da mata da yara kanana kafin gwamnatin Spain ta kai musu dauki.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, sun sha alawashin ci gaba da hadin kai da takwarorinsu na Turai domin rage kwararar bakin da ke isa kasashen nasu.