Isa ga babban shafi
Jamus

Merkel ta cimma matsaya kan hadakar jam'iyyun Jamus

Manyan jamiyyun siyasar Jamus sun cimma yarjejeniyar hadin-gwiwa don kawo karshen tankiyar da ake samu a tsawon watanni 6 tsakanin jamiyyar shugabar gwamnatin kasar, Angela Merkel da jamiyyar Social Democrat.

Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel
Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel REUTERS/Hannibal Hanschke
Talla

Jamiyyun sun fitar da matsayarsu ta karshe da suka bayyana da turbar tsira game da sabaninsu da kuma kasar ta jamus da ke kan gaba a karfin tattalin arzikin Turai, wadda kuma a fayyace za ta bada damar tazarce ga shugaba Merkel a karo na 4 a cewar ministan kudin kasar Peter Altemier.

Shugaba Merkel da ake ganin kwarewarta wajen jagoranci a Turai lura da rawar da ta ke takawa a nahiyar, an lura cewa kuzarinta ya ragu saboda yadda rikicin siyasar kasar da kuma sha’anin batun hadakar ya yi ki ci ya ki cinyewa.

To sai dai ga dukkanin alamu, hadakar ka iya fuskantar cikas lura da matakin shugaban jam’iyyar SPD, Martin Schulz na watsi da tsarin, abin da ya harzuka sauran jamiyyun gabanin zaman karshen da za su yi wanda ake tsammanin anan ne zai bayyana matsayarsa ta bukatar wasu manyan kujeru da suka hada da na kasashen waje da na kudi.

Merkel wadda ta kwashe fiye da shekaru 12 kan mulki na fuskantar matsin lamba ne kan wasu manufofinta da suka hada da na shigar baki kasar da kuma batun ballewar Birtaniya daga Turai.

Cikin zazzafar mahawarar da suka tafka game da manufar shigar baki 'yan gudun hijira, manyan jamiyyun sun ce, za su rage adadadin zuwa dubu 180 daga dubu 220 da aka saba gani a duk shekara.

Kuri’ar baya-bayan nan dai ta nuna farin jinin dukkanin jamiyyun na CDU da CSU ya ragu matuka daga kashi 33 zuwa30.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.