Isa ga babban shafi
Rwanda

Kagame yayi ikrarin samun nasara

Shugaban Kasar Rwanda, Paul Kagame, ya bayyana samun nasara, a zaben shugaban kasar da akayi jiya, bayan sakamakon farko ya nuna cewar, ya samu kusan kashi 93 na kuri’un da aka kirga.Wannan ya sa dubban magoya bayan shugaban sukayi gangami a babban filin wasan Kigali, inda suka fara bukukuwan murna, inda ake ta kade kade da raye raye.Shugaban hukumar zaben kasar, Chryslogue Karangwa, yace shugaba Kagame ya lashe kashi zaben a mazabu 11 daga cikin 30, inda ya samu kuri’u 1,610,422 daga 1,734,671.Masu nazarin siyasar kasar, sun danganta nasarar da cigaban da Rwanda ta samu, ta fannin tattalin arziki da kuma zaman lafiya, a cikin shekaru bakwai na mulkin Paul Kagame.  

Shugaban kasar Rwanda Paul Kagame
Shugaban kasar Rwanda Paul Kagame REUTERS/Finbarr O'Reilly
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.