Gaddafi yana cikin Libya cikin koshin lafiya, inji Arrai TV
Shugaban Gidan Telebijin Arrai na kasar Syria, Mishan al-Juburi Tsohon Dan Majalisar kasar Iraki yace Shugaban Libya Muammar Gaddafi da dansa Saiful Islam suna cikin kasar Libya, bayan ya zanta da shugaban.Mishan al-Juburi ya tabbatar wa Kamfanin Dillacin Labaran kasar Faransa AFP ta Wayar Salula cewa Gaddafi na cikin kasar Libya cikin koshin lafiya kuma baya cikin wani tashin hankali illa cikin farin cikin fatar mutuwa yana yaki.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
An tambaye shi ko ya aka yi ya samu zantawa da Gaddafi, Sai Juburi ya amsa da cewa “idan har ina bukatar Magana da shi, zan tura masa sako ta wayar Salula, idan kuma yana bukatar aikawa da sako shi ke turo mana da sako mu tuntube shi”.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu