Isa ga babban shafi
Kamaru

An rantsar da Paul Biya karo na shida a Kamaru

A yau alhamis ne aka rantsar da Paul Biya a matsayin sabon shugaban kasar Kamaru a karo na shida bayan kammala zaben shugaban kasa a 9 ga Octoba. A ranar 21 ne ga watan Octoba kotun kolin Kamaru ta bayyana cewa Biya ne ya lashe zaben da kuri’u sama da kashi 77 tsakanin shi da abokin hamayyarsa Fru Ndi wanda ya samu kuri’u sama da kashi 10.Tun kafin fitar da sakamakon zaben Fru Ndi tare da sauran ‘yan takara guda shida suka yi watsi da sakamakon zaben tare da kiran gudanar da zanga-zanga domin nuna adawa da sakamon zaben.Kasashen Faransa da Amurka sun lura cewa zaben ya hadu da cikas tare da tabka magudi, sai dai kasar Faransa ta yi fatar a zabuka masu zuwa na ‘yan Majalisu an yi kokarin gudanar da sahihin zabe duk da cewa Alain Juppe Ministan harakokin wajen kasar ya yi na’am da yadda aka gudanar da zaben.  

Shugaban kasar Kamaru Paul Biya lokacin da zai kada kuri'arsa  à Yaoundé.
Shugaban kasar Kamaru Paul Biya lokacin da zai kada kuri'arsa à Yaoundé. REUTERS/Akintunde Akinleye
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.