Libya
Kwamitin Sulhun MDD ya kawar da takunkumin kan kasar Libya
Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya, ya amince da kawo karshen takunkumi wa Babban Bankin kasar Libya da sauran bankuna saka jari na kasar.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Talla
Jami’an diplomasiya sun ce an dauki matakin domin magance matsalolin kudade da kasar ke fuskanta.
Kasar Amurka ta bayyana kawo karshen takunkumin karya tattalin arziki da ta saka wa kasar ta Libya.
Duk matakan an dauka yayin rikicin kasar, domin gurgunta gwamnatin Marigayi Muammar Gaddafi, wanda da aka hallaka bayan mulkin na shekaru 42.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu