Isa ga babban shafi
Libya

Aisha Gaddafi ta bukaci gudanar da bincike kan kisan Mahaifinta

Aisha Ghadafi ‘Yar Marigayi Tsohon shugaban kasar Libya, Muammar Ghadafi, ta bukaci kotun hukunta manyan laifuka kaddamar da binciken yadda aka kashe mahaifinta, da Dan uwanta Mutassim.

Aisha Gaddafi 'yar Tsohon shugaban kasar Libya Mu'ammar Gaddafi
Aisha Gaddafi 'yar Tsohon shugaban kasar Libya Mu'ammar Gaddafi REUTERS/Louafi Larb
Talla

Lauyanta, Nick Kaufman, ya rubuta wasika ga kotun, inda ya bukaci daukar mataki kan yadda aka kashe Ghadafi, ganin yadda ake ta nuna hotunan gawarsa ta Bidiyo a kasashen duniya,

Aisha Ghaddafi tana bukatar  sanin ko kotun zata gudanar da bincike ko akasin haka kamar yadda Lauyanta ke shidawa kamfanin Dillacin labaran Faransa AFP.

An Kashe Gaddafi ne tare da dansa Mutassim bayan da ‘Yantawaye suka kama su a cikin Libya.

A cikin wasikar da lauyan ya rubutawa Kotun yace Moammar Gaddafi da Mutassim an kama su ne da ransu ba tare da yunkurin yin barazana ga rayuwar wani ba, amma aka kasha su tare da nuna gawarsu a bainar Jama’a.

A ranar 27 ga watan Yuni ne kotun Duniya ta ICC ta mika sammacin kamo Muammar Ghaddafi bisa zargin aikata laifukan yaki da cin zarafin bil’adama a lokacin da ake zanga-zangar adawa da gwamnatinsa.

Sai dai har yanzu babu wani tabbaci ko kotun ta samu sakon wasikar.

Yanzu haka Aisha da kannenta Muhammad da Hannibal da maihaifiyarsu Safiya sun samu ‘yancin gudun Hijira zuwa kasar Algeria.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.