Isa ga babban shafi
Rasha-Amurka-Libya

Putin ya zargi Amurka wajen kisan Gaddafi

Fira Ministan kasar Rasha Vladimir Putin yace da hadin gwiwar dakarun Amurka aka kashe tsohon shugaban kasar Libya Kanal Gaddafi ba tare da yanke masa hukunci ba.

Fira Ministan kasar Rasha Vladimir Putin
Fira Ministan kasar Rasha Vladimir Putin REUTERS/Alexsey Druginyn/RIA Novosti/Pool
Talla

A lokacin da ya ke amsa tambayoyin ‘Yan kasar ta gidan talabijin, Fira Ministan ya bayyana amincewarsa da zanga-zangar da ‘Yan adawa suka yi a cikin kasar, don neman soke zaben ‘Yan Majalisu.

A cewarsa idan har zanga-zangar bata kaucewa doka ba, ‘yan kasar na da ‘yancinsu.

Putin yace zai bada umurnin sanya na’urorin daukar hotuna a tashoshin zabe, kafin zaben shugaban kasar da za’ayi a watan Mayun badi, don kaucewa samun irin wannan matsala, amma kuma ya bayyana sakamakon zaben ‘Yan Majalisun a matsayin ra’ayin ‘Yan kasar.

Fira Ministan yace da kansa ya ga yadda aka gudanar da zanga-zangar ta talabijin, inda ya ga matasa na bayyana ra’ayinsu, kuma ya gamsu da haka.

Yau ne ake saran duk masu bukatar takarar shugabancin kasar, su bayyana bukatarsu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.