Isa ga babban shafi
Somalia-Birtaniya

Kasashen duniya sun goyi bayan kawo karshen matsalolin Somalia

Kasashen Duniya sun amince tare da bada goyon bayan samar da hanyoyin yaki da fashin jirgin ruwa da ta’addanci da rikicin siyarar da suka addabi kasar Somalia bayan kammala taro a birnin Landon.

Al'ummar kasar Somalia da ke cikin halin matsananci yunwa da tashin hankali
Al'ummar kasar Somalia da ke cikin halin matsananci yunwa da tashin hankali UN Photo/Stuart Price
Talla

Taron kasashen ya amince da kudirori bakwai da suka kunshi tallafin gaggawa da girke dakarun wanzar da zaman Lafiya na Tarayyar Afrika a Somalia

Sakatariyar Harakokin wajen Amurka Hillary Clinton tace ya zama wajibi kasashen Duniya su hada hannun domin yaki da Al shabeb.

Rikicin Somalia da aka kwashe tsawon shekaru ana gudanarwa ya yi sanadiyar gurgunta al’amurra da ci gaban gwamnatin Somalia.

Kungiyar Al Shabeb da ta fitar da sanarwar aure da Al Qaeda ita ke kula da wasu sassan yankunan kasar.

Sai dai Uwar gida Clinton ta yi watsi da duk wani mataki na tattaunawa da Al Shabeb domin hadewar ta da kungiyar Al Qaeda. A cewar Clinton kawancen Al Shabeb da Al Qaeda ya nuna cewa sun rufe hanyar sasantawa.

Sai dai kuma Taron kasashen ya bude hanyar sasantawa tsakanin bangarorin Somalia domin samun zaman lafiya a kasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.