Isa ga babban shafi
Libya-Mauritania

Mauritania ta karyata yarjejeniyar mika Sanusi tsakaninta da Libya

Gwamnatin kasar Mauritania tace babu wata yarjejeniya tsakaninta da Libya, don mika Abdullahi Sanussi babban na hannun damar Kanal Gaddafi kuma Tsohon shugaban jami’in asiri, bayan kasar Libya ta yi ikirarin cim ma yarjejeniyar da kasar.

Abdullah al-Senussi, Babban na hannun damar Kanal Gaddafi na Libya kuma babban jami'in leken asirin gwamnatin Libya a zamanin Gaddafi wanda hukumomin mauritania suka cafke a watan Agustan bara
Abdullah al-Senussi, Babban na hannun damar Kanal Gaddafi na Libya kuma babban jami'in leken asirin gwamnatin Libya a zamanin Gaddafi wanda hukumomin mauritania suka cafke a watan Agustan bara REUTERS/Paul Hackett/
Talla

Wata majiyar Gwamnatin kasar Mouritania ta shaidawa kamfanin Dillancin labaran Faransa cewa, babu wani alkawali tsakaninta da Libya game da mika Sanussi kamar yadda mataimakin Fira Ministan Libya ya bayyana.

Tuni dai kakakin gwamnatin Libya Nasser al-Manaa, ya shaidawa manema labarai game da cim ma yarjejeniyar da Mauritania bayan ganawa da shugaban kasar Mohamed Ould Abdel Aziz.

Mista Manaa dai yana cikin tawagar kasar Libya da suka kai ziyara Nouakchott domin sasantawa da Mauritania don hannunta Sanussi wanda hukumomin Mauritania suka cafke a filin saukar jirgin kasar akan hanyarsa daga Casablanca na kasar Morroco.

Tun a ranar 27 ga watan Yuni ne kotun hukunta manyan Laifuka ta gabatar da sammacin cafko Sanussi bisa zarginsa da Kisa da keta hakkin bil’adama a gabacin birnin Benghazi.

Akwai dai Tuhume tuhume da ake zargin Sanussi a kasashe n Faransa da Saudiyya da Spain, inda wata majiyar Diflomasiya a kasar Mouritaniya ta bayyana cewa jekadun kasashen sun gana da shugaba Aziz game da Sanussi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.